IQNA

An Rarraba kwafin kur'ani 30,000 a wurin baje kolin littafai na Alkahira

15:04 - February 02, 2023
Lambar Labari: 3488598
Tehran (IQNA) rumfar ma'aikatar kula da harkokin addinin musulunci ta kasar Saudiyya ta raba mujallun kur'ani mai tsarki 30,000 a wurin baje kolin littafai na kasa da kasa a birnin Alkahira.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Al-Bilad cewa, rumfar ma’aikatar kula da harkokin addinin muslunci, da’awah da kuma jagorancin addinin muslunci ta kasar Saudiyya a wajen bikin baje kolin littafai na kasa da kasa karo na 54 na birnin Alkahira ta raba fiye da mujalladi 30 na kur’ani a matsayin kyauta ga maziyartan wannan rumfar.

An rarraba wannan adadin kur'ani ne tun farkon wannan baje kolin a ranar 25 ga watan Janairu.

Wani bangare na rumfar wannan ma'aikatar an sadaukar da shi ne ga cibiyar buga kur'ani mai tsarki ta Sarki Fahd kuma tana ba da juzu'in kur'ani iri-iri tare da fassara cikin fiye da harsuna 76 na duniya.

Hakanan ana gabatar da aikace-aikacen zamani a cikin wannan rumfar, kuma an sanya allo don aikin Hajji da Umrah.

 

4119104

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa:
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
captcha