IQNA

Kungiyar Hadin Kan Musulunci:

Kona makarantar musulmi a Indiya misali ne na kyamar Musulunci

15:49 - April 05, 2023
Lambar Labari: 3488920
Tehran (IQNA) A cikin wata sanarwa da kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta fitar ta bayyana kona wata makarantar Islamiyya a jihar Bihar ta Indiya da kuma wulakanta kur'ani mai tsarki a cikin wannan lamari a matsayin misali karara na kyamar Musulunci da kuma yadda ake ci gaba da cin zarafin musulmi a kasar.

Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar Aljazeera cewa, kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta sanar da cewa, tashin hankalin da mahalarta bikin Ram Navami suka yi, wata alama ce ta kara nuna kyama ga addinin muslunci a kasar Indiya.

Wannan kungiya ta yi Allah wadai da ayyukan ta'addanci da barna a makarantar Islamiyya da ke jihar Bihar.

A cikin sanarwar da wannan kungiya ta fitar, an bayyana cewa, lamarin hare-haren da aka kai kan musulmi a yayin wannan biki na kwanaki 9, wata alama ce ta kara nuna kyama da kiyayya ga al'ummar musulmi a Indiya.

Ma'aikatar harkokin wajen Indiya ta yi Allah wadai da wannan bayani tare da sanar da cewa kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta fara yada farfaganda kan gwamnatin Indiya.

Arindam Bagchi, mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen Indiya, ya yi ikirarin a shafin Twitter cewa: Wannan bayanin wani misali ne na ajandar kyamar Indiya, wanda ke lalata amincinsu.

Kafofin yada labaran cikin gida sun yi nuni da cewa, jerin gwanon mabiya addinin Hindu masu tsattsauran ra'ayi dauke da takuba, sanduna da sauran makamai sun bi ta unguwannin musulmi a garuruwa da dama, suna rera kalamai na nuna kyama tare da kona gidajen musulmi da shaguna a wasu wurare.

Rahotanni daga kafafen yada labarai na kasar sun ce akalla mutane biyu ne suka mutu sakamakon tashin hankalin da aka yi a yayin bikin, ciki har da daya a jihar Bihar, inda hukumomi suka tura daruruwan ‘yan sandan kwantar da tarzoma tare da katse intanet din wayar salula domin hana tada zaune tsaye.

  Kungiyar Hadin Kan Musulunci ta ce tashe-tashen hankula a lokacin bikin ya kai ga kona wata makarantar musulmi da kuma dakin karatu da wata kungiyar masu tsattsauran ra'ayin addinin Hindu ta yi a Bihar. An ba da rahoton irin wannan tashe tashen hankula daga West Bengal, Gujarat, Uttar Pradesh da sauran jihohi, wanda ya kai ga kama sama da 100 a fadin kasar.

Sakatariyar kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta bukaci mahukuntan Indiya da su dauki kwararan matakai kan masu aikata irin wannan aika-aikar da kuma tabbatar da tsaro, hakkoki da mutuncin al'ummar musulmi a kasar.

Masu sukar lamirin sun ce kungiyoyin Hindu masu tsatsauran ra'ayi na ci gaba da cin zarafi kan musulmi tun bayan zaben Narendra Modi da aka zaba a matsayin Firaminista a shekara ta 2014.

 

4131568

 

 

captcha