Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Petra cewa, an gudanar da bikin rufe gasar kur’ani mai tsarki ta Hashimi na kasa da kasa da kuma na kasa baki daya a birnin Amman na kasar Jordan tare da halartar sarki Abdullah na biyu.
A cikin wannan biki, an karrama 'yan kasar Jordan 37 da aka zaba a matakin kasa, da mahalarta 5 na kasa da kasa da kuma mambobin alkalai 9.
A wajen rufe taron da aka gudanar a harabar masallacin Sarki Hossein Bin Talal, an ba wa wadanda suka yi nasara kyautar shaidar yabo da kyaututtuka.
'Yan takara 1000 na kasar Jordan da ’yan takara 43 na kasa da kasa daga kasashen Larabawa da na Musulunci ne suka halarci wannan gasa.
A wannan gasar, Nadi Saad Jaber Muhammad daga Masar, Muhammad Abdul Khaliq Batil daga Canada, Muhammad El Amin Adam Moussa daga kasar Chadi, Abu Bakr Muhammad Bila Jalo daga Kenya, Ezzeddin Omar Ahmed Ibrahim daga Yemen ne suka lashe matsayi na daya zuwa na biyar.
Gasar kasa da kasa ta haddar kur'ani mai tsarki ta kasar Jordan na daya daga cikin gasa mafi dadewa a matakin kasa da kasa, wadda aka fara tun shekara ta 1993 a bisa tsarin sha'awar kur'ani mai tsarki na kasar Jordan da ma'aikatar kula da waqaqa da harkokin addinin musulunci ta wannan kasa.