Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Al-Furqan cewa, bisa sakamakon binciken farko na kwamitin kare hakkin bil’adama na majalisar dattijan kasar Canada mai alhakin gudanar da bincike kan al’amarin kyamar musulmi da cin zarafin musulmi a cikin al’ummar kasar Canada, wannan lamari ya samo asali ne daga wannan kasa.
Kwamitin ya bayyana a cikin wani rahoton cewa, mata musulmi masu sanya hijabi, ciki har da mata bakar fata, su ne suka fi kamuwa da kyamar Musulunci.
A cikin rahoton na wannan kwamiti, an jaddada cewa abu ne mai wahala a magance kyamar Musulunci a bangarori daban-daban na al'umma.
Shugaban kwamitin Sanata Salmi Atollah Jan, ya bayyana haka a wata tattaunawa ta wayar tarho da ya yi da daya daga cikin kafafen yada labarai na kasar Canada: Kasar Canada na fuskantar matsala. Muna jin irin matsaloli da hare-haren wuce gona da iri da al’ummar musulmin kasar nan suka fuskanta.
A cewar Attaullah Jan, wannan matsala ta fi yadda alkalumman da ake nunawa a yanzu; Domin da yawa daga cikin musulmi a fadin kasar Canada na rayuwa cikin tsoron kada a kai musu hari
Alkaluman da hukumar kididdiga ta Canada ta fitar a watan da ya gabata sun nuna cewa laifukan kyamar musulmi da aka kai rahoto ga 'yan sanda sun karu da kashi 71 cikin 100 tsakanin shekarar 2020 zuwa 2021.
Wannan kwamiti ya fara aiki ne a watan Yunin 2021 bayan mutuwar wasu 'yan uwa musulmi hudu a lardin Ontario.