Shafin yanar gizo na Larabci mai lamba 21 ya bayar da rahoton cewa, dakarun da ake kira na daukin gaggawa a Sudan, wanda kwamandansu shi ne Muhammad Daghlo (Hamidati), sun cire kalmar Qudus daga tambarinsu, matakin da ya haifar da martani da dama a shafukan sada zumunta a cikin kwanakin baya.
Yayin da a baya an ga kalmar Quds a karkashin tambarin rundunar, amma tun daga ranar 16 ga wannan wata, an cire wannan kalma daga hotunan tambarin dakarun, wadanda bangare ne daga cikin bangarorin da ke rikicin baya-bayan nan ya barke a kasar Sudan.
Shafin Twitter na rundunar ya cire kalmar Quds daga tambarin ta tun ranar 18 ga watan Afrilu ba tare da bayar da wani bayani kan wannan sauyi ba, kuma wannan sauyin da aka samu kwatsam ya haifar da martani da rudani a tsakanin masu fafutuka ta yanar gizo.
Wani ma’abocin amfani da shafin Twitter mai suna Maher Chawich ya rubuta dangane da haka cewa: Duk da cewa kalmar “Quds” da ke cikin tambarin rundunar dakarun gaggawa gajera amma kuma abin tambaya shi ne dalilin cire kalmar a halin yanzu.