IQNA

Jagoran Juyin Juya Halin Muslunci Na ran Ya Kai Ziyara A Taron Baje Kolin Littafai Na Kasa Da Kasa A Tehran

Tehran (IQNA) Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya kai ziyarar ne a taron baje kolin litattafai na kasa da kasa a birnin Tehran

Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya kai ziyarar ne a taron baje kolin litattafai na kasa da kasa karo na 34 na birnin Tehran babban birnin kasar ta Iran, inda ya bayyana shi a matsayin wani gagarumin taro na karfafa al'adu da yada ilimi a bangarori daban-daban.