IQNA

Dan keken kasar Faransa ya shiga kasar Turkiyya ne a tafiyar Hajjinsa

19:29 - May 23, 2023
Lambar Labari: 3489191
Tehran (IQNA) Dan tseren keken Faransa da Morocco wanda zai je aikin Hajji a keke ya shiga Turkiyya ne a kan hanyarsa.

Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Anatoly cewa, Nabil Al-Nasri wani dan tseren keke dan kasar Faransa da Morocco da ke shirin gudanar da aikin hajjin a keke, ya shiga kasar Turkiyya a lokacin da yake tafiya.

Ya fara tafiyar ne a ranar 22 ga Afrilun bana, ya kuma ratsa kasashe 11 zuwa yanzu.

Wannan mai tuka keke yana neman yin tafiyar Hajjin sa ne bisa tafarkin magabata da musulmi da kuma na da.

A sa'i daya kuma, Nabil Al-Nusri yana kokarin jawo hankalin mutane kan wasu batutuwa da suka hada da dumamar yanayi.

4142721

 

Abubuwan Da Ya Shafa: hajji kasashe hankali tafiya musulmi
captcha