Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na PRN cewa, filayen tashi da saukar jiragen sama na kasa da kasa guda shida a kasar Saudiyya, 4 daga cikinsu suna cikin manyan filayen jiragen sama 100 a duniya. Wadannan filayen jiragen saman za su karbi maniyyata miliyan 1.7 a lokacin aikin Hajji tare da jirage 7700 daga nahiyoyi bakwai. A lokacin aikin Hajji, jiragen sama da yawa na kamfanonin jiragen sama na duniya za su canza hanyarsu zuwa wannan kasa ta Gabas ta Tsakiya.
Kamfanin Jiragen Sama na Saudi Arabiya (GACA) ya samar da kayan aikin filayen saukar jiragen sama na kasa da kasa, musamman filayen saukar jiragen sama masu karbar maniyyata zuwa dakin Allah tare da hadin gwiwar ma’aikatar aikin Hajji. Hudu daga cikin wadannan filayen tashi da saukar jiragen sama an sanya su cikin manyan filayen tashi da saukar jiragen sama 100 a duniya a shekarar 2023, a cewar rahoton Skytrax UK, wanda ya yi nazari kan manyan kamfanonin jiragen sama da filayen jiragen sama 550 a duniya.
Alhazan kasashen waje da suka je Saudiyya ta jirgin sama a shekarar 2019 sun kai kashi 93% na adadin alhazan kasashen waje, wanda ya kai miliyan 1.7. Za a gudanar da wadannan jiragen ne a filin tashi da saukar jiragen sama na Jeddah, da filin jirgin Yarima Mohammed Bin Abdulaziz, da filin jirgin saman Madina, da filin jirgin saman Taif, da filin jirgin saman Prince Abdul Mohsen dake Yanbu, da filin jirgin sama na King Khalid dake Riyadh, da kuma filin jirgin sama na King Fahd dake Dammam.
Dangane da gogewar da ta yi wajen mu'amala da mahajjata, ma'aikatar aikin Hajji ta Saudiyya ta dauki matakan kare lokacin mahajjata. Ma'aikatar ta kaddamar da gangamin wayar da kan jama'a a kasashen da suka fito domin sanin tsarin sufurin jiragen sama na cikin gida, kwastam da ka'idojin fasaha ta hanyar amfani da harsuna 11, da kuma tabbatar da isar da sakonninta ga mutane da dama.
Ministan Hajji da Umrah na Saudiyya Tawfiq al-Rabi'ah ya bayyana cewa, a wani biki a hukumance da ma'aikatar ta gudanar a Jeddah a makon da ya gabata, Saudiyya na shirin kara yawan maniyyata a shekaru masu zuwa. Ya kara da cewa hakan ya yi daidai da manufar kasar Saudiyya ta 2030.