Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, Bayram Aiti daya daga cikin mashahuran malaman kur'ani ya rasu a yau bayan ya sha fama da jinya.
Ya kasance memba a tsangayar ilimin addinin musulunci da ke Novi Pazar a kasar Serbia, wanda ya horar da masu haddar kur’ani da dama a lokacin rayuwarsa.
Bayram Aiti da ne ga marigayi Hafez Rafiq Aiti, daya daga cikin manyan malaman kur'ani a yankin Balkan.