Alkahira (IQNA) An wallafa wani faifan bidiyo na wasu makaratun kasar Masar guda biyu daga karatun Mahmoud Shahat Anwar, matashi kuma fitaccen makarancin wannan kasa, a yanar gizo.
Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, a kwanakin baya Mahmoud Shahat Anwar ya karanta suratul Nazaat a wani taron jama’a a kasar Masar a gaban masoyan kur’ani.