IQNA

Martanin Hamas Ga Sakatare Janar na MDD Kan Kiran Gwagwarmayar Falastinawa Tashin Hankali

16:00 - September 15, 2023
Lambar Labari: 3489820
Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas, yayin da ta yi watsi da bayanan da babban sakataren MDD ya yi a baya-bayan nan game da tsayin dakan da al'ummar Palastinu ke yi da ya kira tashin hankali, ta jaddada cewa hakkinsu ne su kare kansu daga 'yan mamaya.

A rahoton Al-Rasaleh Net, kungiyar gwagwarmayar Islama ta Hamas ta yi watsi da bayanin babban sakataren MDD Antonio Guterres da ya kira gwagwarmayar Falastinawa da tashin hankali, tare da bayyana cewa wannan bayanin bai dace da mai magana kan hakki na bil'adama ba.

Kungiyar Hamas ta kuma kara da cewa ta hanyar fitar da sanarwar cewa tsayin daka na al'ummarmu mataki ne da ke bisa ka'idojin kasa da kasa, kuma wannan tsayin daka wani hakki ne da al'ummar Palastinu ba za su yi kasa a gwiwa ba, kuma za su ci gaba da tinkarar 'yan mamaya na sahyoniyawan har sai sun kawo karshen hakan a ƙasarsu.

A cikin bayanin kungiyar Hamas, an jaddada cewa: tashin hankali da ta'addanci kalmomi ne na ayyukan yahudwa  'yan mamaya na sahyoniyawa da masu mara musu baya, adanda ke da cikakken alhakin tabarbarewar al'amura da kawo cikas ga rayuwar Palasdinawa da tauye musu hakkinsu na kasa.

Hamas ta bukaci Sakatare Janar da Majalisar Dinkin Duniya da su cika aikin da aka ba su na kare hakkin al'ummar Palastinu da kuma yin Allah wadai da 'yan mamaya da cin zarafi da suke ci gaba da yi da kawo karshen laifukansu da wariyar da mamaya, ta yadda al'ummar Palasdinu za su iya amfani da 'yancinsu a cikin kasarsu.

 

 

 

4169047

 

 

captcha