IQNA

Dakarun yahudawan sahyuniya sun killace Masallacin Ibrahimi da ke Hebron

15:43 - September 17, 2023
Lambar Labari: 3489828
Ramallah (IQNA) A karkashin tsarin bukukuwan yahudawa da kuma sabuwar shekara ta yahudawan sahyuniya sojojin gwamnatin sahyoniyawan sun yi wa masallacin Ibrahimi kawanya da ke birnin Al-Khalil tare da rufe kofarsa ga masu ibadar Falasdinu.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar Wafa cewa, Ghassan al-Rajbi daraktan masallacin Ibrahimi da ke birnin Hebron ya sanar a cikin wata sanarwa da ya fitar cewa: An gudanar da wannan aiki ne a cikin tsarin shirin yahudawan sahyuniya na raba wannan wuri mai tsarki .

Haka nan kuma yayin da yake ishara da cewa Isra'ila ta mamaye kusan kashi 36 cikin 100 na guraren wannan masallaci na dindindin, inda ya ce: Makiya yahudawan sahyoniya suna rufe masallacin Ibrahimi da ke Hebron ga Falasdinawa na tsawon kwanaki 10 a kowace shekara tare da hana su yin ibada da salla a wannan masallaci. Wurin ya haramta.

Ghassan al-Rajbi ya ci gaba da cewa: Gwamnatin Sahayoniya ta yanke shawarar rufe masallacin Ibrahimi a ranakun 16, 20, 24 da 25 ga wannan wata.

Idan dai ba a manta ba tun a shekara ta 1994 ne, bayan kisan gillar da aka yi wa Falasdinawa masu ibada 29 a hannun Baruch Goldstein, wani mazaunin sahyoniyawan sahyoniya, gwamnatin yahudawan sahyuniya ke kokarin raba masallacin Ibrahimi na Hebron zuwa bangarori biyu na musamman na musulmi da yahudawa.

 

4169245

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: masallaci khalil falastinu yahudawa killace
captcha