Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Sahra Media cewa, kungiyar ilimi da kimiya da al’adu ta duniya Isesco a ranar Litinin din nan ta amince da yin rijistar wasu sabbin ayyukan tarihi guda uku daga kasar Mauritaniya a matsayin wani bangare na tarihi na addinin muslunci. Kamar yadda Al-Nami Walid Salehi, tsohon gwamnan masarautar Mauritaniya ya ruwaito ta shafinsa na Facebook cewa kabarin Amir na Daular Marabtun, Abu Bakr bin Amer, shi ne masallacin "Katake" da kuma wurin tarihi na "Tukba". .
Masallacin Katake
A tsakiyar tsohuwar unguwar Katake a birnin Kihidi da ke kudancin kasar Mauritaniya, akwai wani tsohon masallaci mai salo na gine-gine na musamman da kuma dogon tarihi wajen yada addinin Musulunci a wannan yanki.
Rahotannin tarihi sun nuna cewa, an gina wannan tsohon masallaci ne a karshen karni na 18 tare da taimakon kudi daga wasu al'ummar yankin da suke gudanar da harkokin kasuwanci a kasashen da ke makwabtaka da su, wanda ya zama masallacin farko mai girman irin wannan a yankin.
Wasu masana tarihi na ganin cewa gine-ginen masallacin ya yi kama da masallacin Timbuktu na Musulunci, wanda za a iya daukarsa a matsayin wurin haduwar al'adun Larabawa, Musulunci da Afirka, kuma ko ta yaya ya zama cibiyar addinin Musulunci a yammacin Afirka. Ya kasance wurin haduwar wayewar Larabawa da Afirka kuma cibiyar addini a yammacin Afirka.
Kabarin Amir Abu Bakr bin Amer
Kabarin Amir Abu Bakr bin Amer ana daukarsa a matsayin daya daga cikin muhimman wuraren ibada a kasar Mauritaniya, domin yana daya daga cikin manya-manyan Marabtun wadanda suka shagaltu da yaki da kuma koyar da fikihu. Wannan Amir Mujahid ya rasu a shekara ta 480 bayan hijira, daidai da 1087 miladiyya.
An san wurin da aka binne shi da sunan Muqsam Boubaker bin Amer kuma gado ne na kasa da aka kebe a cikin jerin jamhuriyar Musulunci ta Muritaniya ta kasa.