IQNA

Yemen: Jiragen Yakin Amurka Da Burtaniya Sun Ci Gaba Da Kai Hare Hare Kan Kasar

15:14 - February 05, 2024
Lambar Labari: 3490589
IQNA -Jiragen yakin Amurka da kumaBurtaniya sun ci gaba da kai hare hare a kan kasar Yemen, inda a hare harensu na safiyar yau Litinin sun cilla makamai masu linzami kan yankunan Saada da kuma Hudaida.

Majiyar talabijin ta Almasirah ta kasar Yemen ta bayyana cewa sojojin Amurka da Burtaniya sun kai hare hare har 15 a kan wadannan yankuna biyu.

Majiyar sojojin kasar ta Yemen ta bayyana cewa hare haren na jiya dai sun hada da wurare 8 a Ras Issa da 3 a Al-zaydiyya a yankin Hudaida sannan wasu 4 a yankin Saada.

Majiyar gwamnatin kasar ta bayyana cewa sun fara wannan yakin ne don tallafawa mutanen Falasdinu da aka zalunta, kuma suna kan wannan shirin, ba zasu kyale jiragen HKI da wadanda suke nufin can wucewa ta babul mandabba. Kuma zasu maida martani kan hare haren da sojojin Amurka da Burtaniya suke kai masu sanadiyyar matsayin nasu.

hausatv

Abubuwan Da Ya Shafa: yemen
captcha