Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na i24news cewa, wani dan kasar Iraqi ne ya aiwatar da kona kur’ani mai tsarki, wanda shi ne karo na biyu da irin wannan lamari. Wannan mutumin a baya ya yi irin wannan aikin kusa da tutar Isra'ila. Saboda haka, waɗannan munanan ayyuka sun tada damuwa a tsakanin ’yan tsirarun addinai na Malmö.
Babban taron malamai na kasashen Turai da kungiyar hadin kan kasashen musulmi a karkashin jagorancin Sheikh Abdulkarim Al-Eisa, sun fitar da sanarwar hadin gwiwa inda suka yi Allah wadai da wannan aika-aika na batanci tare da neman dukkanin al'ummar kasar da su bayyana ra'ayoyinsu cikin mutunci da mutuntawa.
An buga wannan sanarwa yayin da ake gudanar da taron a lokaci guda tare da gasar wakokin Turai (Eurovision) da kuma kara yawan tsaro da jin dadin jama'a a yankin.
Majalisar al'ummar yahudawa a kasar Sweden ta bayyana rashin jin dadin ta kan yadda ake maimaita irin wadannan abubuwa na tunzura jama'a tare da yin kira ga kowa da kowa da ya guji tada zaune tsaye da haifar da kiyayya.
Rabbi Benhas Goldschmidt, shugaban taron malamai na Turai, da Sheikh Al-Eisa a cikin bayaninsu na hadin gwiwa, sun jaddada wajabcin ci gaba da kyautata alaka a tsakanin kungiyoyin addinai daban-daban, musamman a lokutan tashin hankali.
Wannan matakin na haɗin gwiwa tsakanin shugabannin addinai na nuna ƙoƙarin da ake yi na inganta zaman tare da mutunta juna a Malmö, birni mai tarihi da aka sani da bambancin al'adu da addini.
Rabbi Moshe David HaKohin, tsohon shugaban kungiyar Beit Midrash a arewacin Turai, ya yaba da dangantakar da ke tsakanin shugabannin addinin Yahudawa da na Musulmi da kuma muhimmancinta wajen rage zaman dar-dar, musamman ma kafin wani taron da ke da muhimmanci kamar gasar wakokin Turai.
Haɗin kai tsakanin waɗannan ƙungiyoyi wani sako ne mai ƙarfi na adawa da ayyukan da ke da nufin wargaza haɗin kan al'umma tare da jaddada cewa makomar zaman lafiya ta dogara ne kan ci gaba da tattaunawa da mutunta juna, nesa da duk wani aiki na tsokana ko cin zarafi ga kowane addini.
https://iqna.ir/fa/news/4213765