IQNA

Sakon ta'aziyyar jagoran juyin juya halin Musulunci a Iran da kuma sanar da makoki na kwanaki 5

Raisi mutum ne da bai san gajiya ba

14:46 - May 20, 2024
Lambar Labari: 3491184
IQNA - Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei a cikin sakon ta'aziyyar shahadar shugaban kasar Iran da abokan tafiyarsa da kuma bayyana zaman makoki na kwanaki 5 na al'umma ya ce: Shugaban kasa mutum ne da bai san gajiya ba. A cikin wannan lamari al'ummar Iran sun rasa wani bawa mai gaskiya kuma mai kima.

Raisi mutum ne da bai san gajiya ba

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a cikin wani sakon da ya aike kan shahadar Hojjat-ul-Islam Wal-Muslimin Sayyid Ibrahim Raisi, jagoran juyin juya halin musulunci na Iran Ayatullah Khamenei ya sanar da cewa, yana mika ta'aziyyar rashin Dakta Amir Abdollahian, Ministan Harkokin Waje, Hojjat-ul-Islam Wal-Muslimin Al-Hashem, wakilin Babban Malamin Shari'a a Gabashin Azarbaijan, Dr. Rahmati Gwamnan lardin Azarbaijan ta gabas, tare da abokan tafiyarsu.

 Sakon ta'aziyyar Jagoran juyin juya halin Musuluncin shi ne kamar haka;

 da sunan Allah

 Ga Allah Muke Kuma Mu Zuwa Ga Allah Za Mu Koma

 Cikin tsananin bakin ciki da damuwa na samu labarin shahadar Mujahid, shugaban jama'a da kwazon aiki, mai hidima ga ga Imam Ridha (AS) Haj sayyid Ibrahim Raisi, tare da abokan tafiyarsa.

 Wannan mummunan lamari ya faru a lokacin ƙoƙarin hidima; Duk tsawon wa'adin wannan kishin kasa, walau a cikin kankanin wa'adin mulkin shugaban kasa ko kuma kafin nan, ya karar da gaba daya kokarinsa wajen yi wa al'umma hidima da kasa da Musulunci.

Raisi bai san gajiya ba. A cikin wannan mummunan lamari da ya faru al'ummar Iran sun rasa wani babban jigo mai gaskiya kuma mai kima. Ya fifita jin dadin jama’a da yardar  Allah a kan komai, don haka bacin ransa kan rashin godiya da izgilin wasu bai hana shi aiki dare da rana wajen inganta al’amura ba.

 A cikin wannan lamari mai tsanani, fitattun mutane irin su Hajjat ​​al-Islam Al Hashem, mashahuri kuma amintaccen limamin Juma'a na Tabriz, Amir Abdullahian, Mujahidi kuma ministan harkokin waje na kasar Iran, Malik Rahmati,  mai kokari a lamarin juyin juya halin musulunci kuma mai tsoron Allah, kuma gwamna Gabashin Azabaijan, da tawagar jirgin da sauran abokan tafiyarsu, sun shiga cikin rahamar Ubangiji.

 Ina sanar da kwanaki biyar na zaman makoki na jama'a tare da mika ta'aziyyata ga al'ummar Iran. Kamar yadda doka ta 131 ta kundin tsarin mulkin kasar ta tanada, Mokhbar ne zai ci gaba da rike mukamin shugabancin bangaren zartarwa, kuma ya zama wajibi tare da hadin gwiwa da shugabannin majalisun dokoki da na shari'a ya shirya zaben sabon shugaban kasa cikin kwanaki hamsin.

 Daga karshe ina mika ta'aziyyata ga Mahaifiyar Raisi da mai dakinsa da sauran danginsa, da kuma iyalan abokan tafiyarsa, ina kuma addu'ar Allah ya jikansu da rahama. Allah ya bada Hakuri ga iyalan wadanda suka rasu.

 

4217013

 

 

 

 

captcha