Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, masu fafutukar kula da kur’ani da sauran jama’a ne suka gudanar da gangamin na kammala kur’ani mai tsarki da kuma bayar da ladarsa ga ruhin shugaba shahidi da mukarrabansa.
Wannan yunkuri an shirya shi ne domin nuna godiya ga kokarin Ayatullah Sayyid Ibrahim Raisi, kuma kowane mutum zai karanta akalla shafi daya na kur’ani mai tsarki.
Don haka, mutanen da suke son shiga wannan shiri na kur'ani kur'ani suna iya komawa zuwa wojohat.com/313-2/ kuma su karanta ayoyin da suka dace.