IQNA - A safiyar ranar 23 ga watan mayu ne gawar marigayi Ayatullah Sayyid Ibrahim Raisi ta isa birnin Birjand, kuma al'ummar wannan birni sun yi bankwana hadimin Imam Ridha (AS) a wani gagarumin biki. Bisa jadawalin da aka sanar, kafin sallar Maghrib, an kai gawar shahid Raisi zuwa masallacin Mashhad da hubbaren Radhawi , kuma an binne shi a wannan hubbare na Radhawi.