Majalisar Dinkin Duniya ta amince da daftarin kudiri na ayyana ranar 11 ga watan Yuli a matsayin ranar tunawa da kisan kiyashi a Srebrenica.
An fara zaman kada kuri'a ne da shiru na minti daya ga Ayatullah Sayyid Ibrahim Raisi, shugaban kasar Iran da mukarrabansa.
An amince da daftarin kudurin da Jamus da Rwanda suka gabatar da kuri'u 84 na amincewa.
Wannan kudiri dai ya samu kuri'u 68 da kuri'u 19 suka ki amincewa.
Idan dai za a iya tunawa sojojin Sabiya karkashin jagorancin Ratko Mladic sun shiga Srebrenica a ranar 11 ga watan Yulin 1995, bayan da Majalisar Dinkin Duniya ta ayyana yankin Bosnia a matsayin wani yanki mai tsaro, inda suka fara kashe al'ummar wannan birni.
Sojojin Sabiya sun kashe 'yan Bosniya sama da 8,000 tsakanin shekaru 7 zuwa 70 a cikin 'yan kwanaki.