IQNA

Sayyid Hasan Nasrallah:

Ya Kamata Duniya Ta Farka Bayan Mummunan Laifin Yaki A Kan Rafah

15:37 - May 29, 2024
Lambar Labari: 3491242
IQNA - A wajen taron jana'izar mahaifiyarsa, babban sakataren kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon ya bayyana cewa, laifin yaki yaki da aka aikata a Rafah ya kawar da duk wani dalili na karya yana mai cewa: Wajibi ne wannan laifin ya farkar da dukkan mutane da suka yi a duniya.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Ahed cewa, Sayyid Hassan Nasrallah babban sakataren kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon ya bayyana cewa: “Ban samu damar halartar jana’izar mahaifiyata da ta rasu ba. Wajibi na ne in kasance a gaba, amma yanayin tsaro ya hana ni yin hakan.

Ya kara da cewa: Ina jin kasantuwar ku, ina kaunar wannan kasantuwar kuma ina alfahari da shi. A madadin mahaifina da ’yan’uwa maza da mata da kuma a madadin iyalan Nasrallah da Safiuddin, ina mika godiya ta ga kowa da kowa da ya tausaya mana.

Sayyid Nasrallah ya ci gaba da cewa: Daga dukkan wadanda suka fito daga kasashen Lebanon, Iraki, Falasdinu, Iran, Siriya, Pakistan, Turkiyya, Yemen, Bahrain, Kuwait, Masar, Tunisiya, Muritaniya da sauran kasashen Afirka, Jordan da Djibouti da kuma Labanon da ke zaune a kasashen waje wadanda suka  bayyana ta'aziyyarsu, na gode.

Ya kara da cewa: Ina godiya ga 'yan uwana na kungiyar Hizbullah da kuma kungiyar Amal da suka kasance tare da mahaifina tun daga sa'o'i na farko don yin ta'aziyya tare da tsayawa na tsawon sa'o'i da yawa don karbar ta'aziyya. Ina mika godiyata ga iyalan shahidan da suka aiko mana da sakon ta'aziyya

A wani bangare na jawabin nasa, babban sakataren kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon ya yi tsokaci kan laifukan baya-bayan nan da gwamnatin sahyoniyawa  ta aikata a birnin Rafah da ke kudancin zirin Gaza inda ya ce: Kisan kiyashin na Rafah ya nuna irin zaluncin da makiya suke aikatawa da mummunan kudirin da suke da shi.

" Muna fuskantar abokan gaba da ba su yarda da kowace ɗabi'a ko ‘yan adamtaka ba,  sun fi na ‘yan Nazi muni. Mummunan laifin da suka  aikata na Rafah ya kamata ya farkar da duk wani lamiri na masu yin  shuru da nuna halin ko in kula a duniya kana bin da yake faruwa a Gaza.

Nasrallah ya ci gaba da cewa: Laifin Rafah ya kawar da duk wani abin da ake rufa-rufa a kansa da kirkiro dalilai na karya domin kare Isra’ila.

 

4218940

 

 

captcha