Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo nacibiyar hubbaren Imam Ali cewa, Haider Abdul Wahab, mai kula da aikin yin ado na haramin ya bayyana cewa: Sashen tela na shirya bakaken tutoci da tutoci da za su lullube hubbaren a daidai lokacin da Muharram ke gabatowa, domin makokin shahadar Imam Husaini (AS).
Ya kara da cewa: Wannan aikin ya hada da dinki kyallayen guda hudu na kabari mai tsarki, babbar tutar farfajiyar dakin hubbaren, da guda biyu na hasumiya , da tutoci takwas da za a saka sauran bangarori.
Abdul Wahab ya jaddada cewa an shirya tare da sanya tutoci masu rubuce-rubuce na musamman a cikin dakin hubbaren domin watan Muharram da kuma shahadar Imam Hussain (AS).
Har ila yau, barandar zinariya an lulluɓe ta da babbar tuta mai tsayin mita 15 x 14. Har ila yau, za mu sanya bakaken tutoci 77 masu tsawon mita 9 x 1 ciki da wajen wurin ibada.
Al-Khadim ya kara da cewa: Za a dora manya-manyan tutoci 10 a ciki da wajen haramin, baya ga tutoci 21 a cikin lungunan waje, da kuma tutoci 36 a cikin layukan ciki, kowannensu ya kai mita hudu da mita daya, sannan kuma za a dora tutoci 55 a kan ginshikan waje.
A karshe ya ce: Haka nan an tanadar da rubuce-rubuce guda 10 na kofofi guda 10 na hubbaren, wadanda aka rubuta kalmomin “Assalam Alaik ya Amirul Muminin.