IQNA

Taron karrama mata masu karatun kur'ani a kasar Morocco

15:50 - July 20, 2024
Lambar Labari: 3491548
IQNA - Bidiyon muzaharar karrama matan da suke karatun kur'ani a birnin Shishaweh na kasar Maroko ya dauki hankula sosai daga masu amfani da shafukan sada zumunta.

Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Yeni Shafaq al-Arabiya cewa, faifan bidiyo na muzaharar karrama mata masu haddar kur’ani a birnin Shishawe da ke kusa da babban birnin kasar Moroko, ya samu karbuwa daga masu amfani da shafukan sada zumunta daban-daban.

Ayyukan kur'ani na mata sun fadada sosai a kasar Maroko a 'yan shekarun nan.

 Babban bangare na wadannan ayyuka sun hada da kafa cibiyoyin haddar kur'ani, da gudanar da gasar kur'ani mai tsarki da kuma farfado da cibiyoyin kula da kur'ani na gargajiya a yankuna daban-daban na kasar ta Maroko karkashin kulawar ma'aikatar kula da harkokin ilimi ta kasar.

 

 

 
 

 4227538

 

 

captcha