IQNA

Karatun suratul Fajr na kungiyar Tasnim

14:03 - July 30, 2024
Lambar Labari: 3491610
IQNA - Matasan kungiyar yabon tasnim sun karanta ayoyin karshe na suratul fajr bisa tsarin karatun kur'ani na sheikh Abdul basit.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, an sake gabatar da wani sabon shiri na matasan kungiyar rera wakokin kur’ani mai tsarki da kungiyar Tasnim, wadanda ake yawan watsa wasanninsu a kafar sadarwar Poya a sa’o’i kadan kafin kiran sallah.

Wannan sabon aiki an sadaukar dashi ne ga kungiyar karatun ayoyin karshe na suratul Mubaraka Fajr. Karatun wadannan ayoyi ya dogara ne akan shahararriyar karatun Ustaz Abdul Basit.

Ya kamata a lura cewa ƙungiyar waƙar yabo da Tasnim suna aiki a cikin ƙungiyoyin shekaru biyu, manya da matasa. Wannan rukunin yana samar da ayyukan addini ta hanyar studio.

 

 

4229002

 

 

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: karatu karatun ku’ani ayoyi karanta matasa
captcha