IQNA - A cikin wannan faifan bidiyo za ku ga lokacin ganawar karshe da Ismail Haniyeh shugaban ofishin siyasa na kungiyar Hamas da Jagoran juyin juya halin Musulunci a ranar Talatar da ta gabata 9 ga Yuli 2024.

Bayanin tattaunawar da Isma'il Haniyya yayi da jagoran jamhuriyar musulunci ta Iran shine kamar haka;
Duniya haka take, Allah yana karbar rayuwar kuma yana rayawa. Allah madaukakin sarki yana rayawa da matarwa. Amma al'ummar musulmi in Allah ya yarda za ta kasance a raye.
A cewar wani mawaki , idan babban mutum ya rasu, wani babban mutum ne zai maye gurbinsa.
Allah ya kara muku lafiya da nisan kwana. Da yaddar Allah