Kamar yadda Iqna ta ruwaito daga shafin sadarwa na yanar gizo na "Shafaq News" cewa, ma'aikatar harkokin cikin gidan kasar Iraki ta fitar da sanarwa a yammacin yau 8 ga watan Agusta game da kame 'yan kungiyar ISIS 11 da suka hada da wata mata da daya daga cikin shugabannin wannan kungiyar ta 'yan ta'adda da ake yi wa lakabi da "Abubakar" a wurare daban-daban.
A dangane da haka Moqdad Miri, kakakin ma'aikatar da kuma sashin yada bayanan jami'an tsaron kasar Iraki ya bayyana cewa: Rukunin hadin gwiwa na sashen 'yan sanda na lardin Ninawa bayan tattara bayanai da ci gaba da bibiya tare da hadin gwiwar 'yan kasar, sun samu nasarar cafke mutane 11 na wadanda ake zargi a karkashin dokar yaki da ta'addanci cikin sa'o'i 72 da aka kama
Miri ya ce: Daga cikin mutanen da aka kama har da wata mace da daya daga cikin shugabannin ISIS.
Ya ci gaba da cewa: Wadannan mutane sun yi aiki a cikin wannan kungiya a lokacin da kungiyar ta'addanci ta Da'ish ta mamaye birnin Mosul.