A karshen makon da ya gabata ne aka fara gudanar da gasar haddar kur'ani mai tsarki karo na 44 a kasar Saudiyya a kusa da masallacin Harami, kuma za a ci gaba da gudanar da gasar har zuwa karshen watan Agusta inda za a samu halartar Muhammad Hossein Behzadfar da Mohammad Mahdi Rezaei masu haddar Al-kur'ani mai tsarki daga Jamhuriyar Musulunci ta Iran.
Ana gudanar da waɗannan gasa a matakai biyu na farko don tantancewa da matakin karshe. An fara gasar share fage ne a karshen makon da ya gabata kuma duk wanda ya yi nasara a gasar share fage, zai bayyana a mataki na gaba karshe bayan kwana daya ko biyu.
A safiyar ranar 12 ga watan Agusta Muhammad Hossein Behzadfar mahalarci a fagen haddar kur'ani mai tsarki ya halarci matakin share fage na wannan gasa tare da amsa tambayoyi biyar na alkalai.
A wannan mataki, an tambayi wakilin kasar Iran tambayoyi biyar masu rabin shafi. Wadannan tambayoyi suna da alaka da ayoyi daga surorin Nisa'i masu albarka da Taubah da Nahl da Shuara da Hadid da Behzadfar ya amsa dukkan tambayoyin guda biyar ba tare da wata matsala ba.
Ana sa ran Mohammad Hossein Behzadfar zai yi gasa a mataki na gaba a ranakun Talata ko Laraba bayan ya tsallake matakin share fage.
Mohammad Mahdi Rezaei, dayan wakilin kasar Iran , har yanzu bai gudanar da gasarsa a matakin farko ba.
A cewar masu shirya wannan gasa, mahalarta 174 daga kasashe 123 ne suka halarci wannan gasa.