Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Al-alam cewa, ya nadi wadannan hotuna ne ta hanyar kasancewa a titin Al-Souq da kuma shirya rahoto a kai. Titin da aka ambata na daya daga cikin muhimman titunan birnin Beit Lahia da ke arewacin Gaza, wanda sojojin yahudawan sahyoniya suka lalata.
Ta hanyar yin zane-zane a bangon gidajensu da aka lalata a wannan titi, Falasdinawa sun godewa Yemen bisa goyon bayan da take baiwa kasar Falasdinu.
A daya daga cikin rubuce-rubucen bangon, ana iya ganin maudu'in "#Ana-Aliman" (Ni Yemen) wanda ke nuna zurfin da tarihin alakar da ke tsakanin Yaman da Falasdinu.
Wadannan take-take da rubuce-rubucen bango ba komai ba ne illa alakar 'yan uwantaka da ke tsakanin Yaman da Palastinu, wanda kungiyar Ansarullah ta tabbatar a cikin jarumtakar da take yi da gwamnatin yahudawan sahyoniya a cikin tekun Bahar Rum da kuma cikin zurfin kasar Palastinu da ta mamaye.