Kamfanin dillancin labaran iqna daga Thailand ya habarta cewa, a cikin wannan biki, baya ga karrama wadanda suka lashe gasar kur’ani mai tsarki ta kasar Thailand, an yaba wa mambobin kwamitocin addinin muslunci da limaman jama’ar da suka nuna kwazo ta hanyar ba da kyaututtuka da allunan girmamawa.
An fara bikin ne da karatun kur'ani mai tsarki, a lokaci guda kuma an fassara ayoyin zuwa harshen Thai ga sarki.
Daga nan sai sarki da sarauniyar Patani suka ziyarci baje kolin mai taken "Bari makaranta ta horar da mutanen kirki domin kasar" da ma sauran ayyuka.