IQNA

Ayatullah Khamenei: Kasantuwar Amurka a gabas ta tsakiya shi ne tushen dukkanin matsalolin yankin

15:25 - October 02, 2024
Lambar Labari: 3491966
IQNA – Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana kasancewar Amurka a matsayin tushen matsalolin da ke faruwa a yankin.

Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya bayyana a wannan Laraba cewa: Tushen matsalolin da ke faruwa a yankin shi ne kasancewar bakin haure kamar Amurka da wasu kasashen Turai da ke ikirarin neman zaman lafiya na karya.

Jagoran ya bayyana hakan ne a wata ganawa da yayi da jiga-jigan masu fada aji a babban birnin kasar Iran.

"Idan suka kawar da tasirinsu mai cutarwa daga wannan yanki, ba tare da shakka ba, wadannan rikice-rikice, yake-yake, da tashe-tashen hankula za su bace gaba daya," in ji shi, ya kara da cewa, "kasashen yankin za su iya tafiyar da harkokin kasashensu da yankin baki daya da kansu, a cikin zaman lafiya da kwanciyar hankali."

Ayatullah Khamenei ya ce, yayin da yake magana kan Sayyid Hasan Nasrallah, babban sakataren kungiyar Hizbullah, ya ce: "Ina da wasu bayanai dangane da al'amuran kasar Lebanon da kuma batutuwan da suka shafi wannan shahidi mai girma kuma abin kaunarsu, wanda zan yi bayani nan gaba kadan idan Allah ya yarda.

Jagoran ya kara da cewa " nan ba da jimawa ba zan yi magana kan batutuwan Gaza da kasar Lebanon."

Taron dai na zuwa ne kwana guda bayan da dakarun kasar Iran suka kaddamar da Operation True Promise II, inda suka kai hari kan cibiyoyin soji da jami'an tsaron Isra'ila, a matsayin martani ga kisan gillar da Isra'ila ta yi wa shugaban Hamas Ismail Haniyeh, shugaban Hizbullah Nasrallah, da kwamandan IRGC Abbas Nilforoushan.

 

 

4240134

 

 

 

 

captcha