Tashar Al-Manar ta bayar da rahoton cewa, kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon ta sanar da Sheikh Naim Qassem a matsayin sabon babban sakataren kungiyar.
A cikin bayanin kungiyarta Hizbullah ta kasar Labanon ta bayyana cewa: A bisa imani da Allah Madaukakin Sarki, da sadaukar da kai ga sahihiyar hanya ta muslunci bisa koyarwar manzon Allah Muhammad (S.A.W) da riko da ka'idoji da manufofin Hizbullah da kuma tsarin da aka amince da zaben babban sakataren kungiyar, Majalisar shura ta Hizbullah ta zabi Sheikh Naim Qasim a matsayin Babban Sakatare. Hizbullah tana rokon Allah Madaukakin Sarki da Ya taimake shi da karfin gwiwa wajen gudanar da kyakkyawan aiki na jagorancin Hizbullah da gwagwarmayar a tafarkin Musulunci.
Har ila yau, Hizbullah ta kara da cewa: Muna rokon Allah Madaukakin Sarki da daukaka ruhin babban shahidi ma mafi daukaka da daraja Sayyid Hassan Nasrallah (Allah ya kara masa rahma) da shahidai da mayakan gwagwarmayar Musulunci da al'umma masu tsayin daka, masu hakuri da aminci, tare da kara jaddada cewa kungiyar Hizbullah tana nan kan manufofinta har zuwa cimma nasara da yardarm Allah.
Sheikh Naim Qassem shi ne mataimakin babban sakataren kungiyar Hizbullah tun shekara ta 1991, kuma ya kasance cikin wadanda suka kafa kungiyar "Amal" tare da Imam Musa Sadr, da kuma kafa kungiyar Hizbullah a kasar Lebanon.