Kamar yadda gidan talabijin na Aljazeera ya ruwaito, faifan sautin da aka nada aka kuma danganta shi ga Shahid Sinwar, an yada shi sosai a shafukan sada zumunta a ‘yan kwanakin da suka gabata, kuma masu amfani da shi sun yaba karatun da suka ji, amma shin da gaske ne muryar Shahid Yahya Sinwar?
Dangane da haka, sashin tantancewa na tawagar bincike na Al Jazeera Mubasher ya sanar da cewa: Muryar da aka nada da ake yadawa tsakanin masu amfani da sunan Yahya Sinwar tana karatun kur'ani ba ta Yahya Sinwar ba ce.
Aljazeera Mubasher ya ci gaba da cewa: Wannan sautin da aka buga shi ne karatun ayoyi na suratu Mubaraka Ahzab wanda Khalad ya ruwaito daga Hamza da muryar Nasser Al-Saeed, wani matashin makaranci dan kasar Masar.
Ga wannan karatu da aka fitar tare da muryar Nasser Al-Saeed: