Shafin yanar gizo na gidan rediyon Algiers ya bayar da rahoton cewa, kungiyar hadin kan kasashen musulmi daga birnin New York a cikin wata sanarwa da ta fitar a wannan Alhamis a agogon kasar ta Amurka, ta sanar da cewa: Matakin wuce gona da iri na gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila, wani lamari ne da ya saba wa dokokin kasa da kasa da kuma kundin tsarin mulkin majalisar dinkin duniya, tare da keta hurumin kasa mai 'yanci.
Har ila yau, kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta yi kakkausar suka ga cin zarafi da cin mutuncin kasar Jamhuriyar Iraki da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila ta yi, inda ta yi amfani da sararin samaniyar wannan kasa wajen aiwatar da wani mataki na wuce gona da iri kan Jamhuriyar Musulunci ta Iran.
Wannan kungiya ta jaddada cewa Jamhuriyar Musulunci ta Iran da sauran kasashen da abin ya shafa suna da hakki na kare 'yancin kasashensu da yankinsu, da tsaron al'ummarsu kamar yadda dokokin kasa da kasa da kundin tsarin mulkin MDD suka tanada.
Kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta sake yin gargadin cewa laifuffukan da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila ke ci gaba da yi a yankunan Falasdinawa da ta mamaye musamman a Gaza da Lebanon da kuma munanan ayyukanta a yankin na barazana ga zaman lafiya a daukacin yankin gabas ta tsakiya.
Wannan kungiya ta yi kira ga kwamitin sulhu na MDD a matsayin wanda babban alhakin wanzar da zaman lafiya da tsaro na kasa da kasa ya rataya a wuyansu, da ya gagaguta daukar matakain takawa Haramtacciyar kasar Isra'ila birki kan kisan kiyashin da take a Gaza, da kuma hare-haren da take kaiwa kan kasar Lebanon.