Ahmad Abul Qasimi makaranci na duniya ya karanta aya ta 139 zuwa ta 148 a cikin suratu Ali-Imran.
An yi wannan karatun ne a sansanin kwana daya na "Ayarin Al-Qur'ani na Shahidai na Juriya" wanda ya kunshi tsofaffin sojoji, farfesoshi, malamai, masana, manajoji da masu fafutuka. An shirya wannan sansani ne bisa kokarin majalisar koli ta kur'ani tare da hadin gwiwar kungiyar Darul-Qur'an-ul-Karim.