A cewar al-Mayadeen, kafafan yada labaran gwamnatin sahyoniyawan sun sanar da cewa an gano gawar Tzvi Kogan, wani malami da yahudawan sahyoniyawan da ya bace a Hadaddiyar Daular Larabawa.
Ofishin Benjamin Netanyahu, firaministan gwamnatin Haramtacciyar Kasar Isra'ila sahyoniyawan ya kuma tabbatar da gano gawar wannan malamin.
Ofishin Netanyahu ya sanar da cewa: Kisan wannan Malamin lamari ne da ya shafi tsaro na kyamar Yahudawa kuma za mu yi iya kokarinmu wajen zakulo wadanda suka aikata wannan lamari.
Shafin yanar gizo na jaridar yahudawan sahyoniya "Yediot Aharnot" ya kuma rubuta game da hakan cewa hukumomin leken asiri na gwamnatin sahyoniyawan suna hada kai da hadaddiyar daular larabawa domin gudanar da bincike kan wannan lamari da ba a saba gani ba.
Iyalan wannan malamin yahudawan sahyoniya sun sanar da cewa sun daina hulda da shi a ‘yan kwanakin nan, yayin da ake ci gaba da kokarin gano inda yake.
Malamin yahudawan sahyoniya daya ne daga cikin hafsoshin sojojin "Givati" a cikin sojojin yahudawan sahyoniya.
Malamin da aka ce shi ma memba ne na kungiyar Chabad. Wannan kungiya ce mai tsattsauran ra'ayi da ke son korar dukkanin Falasdinawa kuma ba ta yarda da kasancewarsu a ko'ina a cikin Falasdinu ba. A lokacin yakin kisan kiyashi da aka yi a zirin Gaza, wannan kungiya ta taka rawar gani wajen tallafawa sojojin gwamnatin sahyoniyawan da kuma tara musu taimakon kudi, sannan ta bukaci a sake gina matsugunnai a Gaza. "Gidan Chabad na farko a Gaza" ita ce kalmar da 'yan mamaya suka rubuta a kan wani gida a Beit Hanoun.