IQNA

Wasu gungun masu dauke da makamai sun yi awon gaba da kayayyakin da ke hubbaren  Sayyida Zainab a  Siriya

16:17 - December 09, 2024
Lambar Labari: 3492352
IQNA - Kamar yadda faifan bidiyon da aka wallafa ya nuna,  wasu kungiyoyin masu dauke da makamai a kasar Siriya sun kai hari a hubbaren Sayyida Zainab (AS) inda suka yi awon gaba da kayayyakin wannan hubbare mai tsarki.

Shafin yada labarai na Sabrin Telegram ya bayar da rahoton cewa, ta hanyar fitar da faifan bidiyo da dama, an nuna harin da 'yan tawaye suka kai a hubbaren Sayyida Zainab (AS) da ke birnin Damascus da kuma sace-sacen kayayyakin da ake yi na wannan wuri.

A yayin da 'yan tawayen suka kama iko da Siriya sun yi ikirarin cewa ba za su mutunta hubbaren Sayyida Zainab (AS) ba.

 

 

 

 

 

 

4253015

 

 

captcha