IQNA

Ana gudanar da taron kolin Falasdinu na kasa da kasa a kasar Switzerland

16:48 - December 24, 2024
Lambar Labari: 3492441
IQNA - A watan Maris din shekarar 2025 ne za a gudanar da taron kasa da kasa kan matsayin Palastinu a kasar Switzerland tare da halartar kasashen da ke cikin yarjejeniyar Geneva.

Shafin yanar gizo na minanews ya habarta cewa, za a gudanar da wannan taro ne a karkashin kulawar gwamnatin kasar Switzerland, kuma ana sa ran zai haifar da sakamako da dama na siyasa da kuma bukatu na haramtawa gwamnatin sahyoniyawan makamai.

Majalisar Dinkin Duniya ta bai wa gwamnatin kasar Switzerland izinin gudanar da wannan taro da zai mai da hankali kan kare fararen hula da kuma batun mamayar da Isra’ila ke yi a yankunan Falasdinawa da kuma nauyin da ya rataya a wuyan kasashe daban-daban a wannan fanni.

Switzerland ita ce ƙasa mai sa ido kan Yarjejeniyar Geneva kuma tana taka muhimmiyar rawa wajen kiyaye takaddun yarjejeniyar ta asali kuma tana yin tsaka tsaki a cikin rikice-rikice tare da tallafawa kasashen da suka sanya hannu kan yarjejeniyoyin.

Ya zuwa yanzu dai an gudanar da taruka uku kan Falasdinu a kasar Switzerland a shekarun 1999, 2001, da 2014, kuma taron na 2014 ya gudana ne bayan yakin kwanaki 50 da Isra'ila ta yi a zirin Gaza.

A cikin tarukan biyu na farko, kasashe mambobin yarjejeniyar Geneva sun bukaci aiwatar da yarjejeniyar Geneva ta hudu a yankunan da aka mamaye ciki har da gabashin birnin Kudus.

Yarjejeniyar Geneva ta hudu ta kare fararen hula da ke karkashin ikon sojojin Haramtacciyar kasar Isra'ila  a yankunansu ko yankunan da aka mamaye, kuma sashe na 49 na wannan yarjejeniya bai bai wa kasar da ke mamaya damar tilasta wa farar hula yin hijira ko kaura zuwa yankunan da aka mamaye ba ko kuma kwashe mutanen da ke da kariya daga mamayar yankuna

Taron kolin na Switzerland ba zai iya yanke shawarwari masu ma'ana ba, amma zai iya karfafa dokokin jin kai na kasa da kasa kan Falasdinu da kuma nauyin da ke wuyan kasashen da ke cikin yarjejeniyar Geneva na yanzu.

 

 

4255888

 

 

captcha