IQNA- Filin wasan motsa jiki na Camille Chamoun da ke wajen birnin Beirut ya samu halartar dimbin magoya bayan adawa da suka taru a wurin domin halartar jana'izar tsohon babban sakataren kungiyar Hizbullah Sayed Hassan Nasrallah da wani dan Hizbullah Sayed Hashem Safieddine.
A cewar majiyoyin na Lebanon, sama da mutane 400,000 daga sassan kasar Lebanon da kuma wasu kasashe sama da 70 ne suka zo domin halartar jana'izar.