Jagora Ya Halarci Taron Al-Kur'ani A Tehran Ranar Farkon Watan Ramadan
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na iqna cewa, a ranar 2 ga watan Maris din shekarar 2025 ne aka gudanar da taron karatun kur’ani mai tsarki na Imam Khumaini Husaini a birnin Tehran na kasar Iran a gaban jagoran juyin juya halin musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei.