IQNA

Maraba da Maulidin Manzon Allah (SAW) da aka yi a kasar Turkiyya

16:52 - April 22, 2025
Lambar Labari: 3493137
IQNA - An gudanar da bikin maulidin Manzon Allah (SAW) na shekara shekara a birnin Diyarbakir na kasar Turkiyya, tare da halartar manyan baki daga kasashen waje.

Kamfanin dillancin labaran İLKHA ya habarta cewa, birnin Diyarbakir na kasar Turkiyya ya dauki nauyin gudanar da taron maulidin al-Nabi (AS) na shekara, wanda ya samu halartar wasu baki daga ciki da wajen kasar ta Turkiyya. Musulmi daga kasashe daban-daban, irin su Arewacin Macedonia da Habasha, sun halarci bikin, inda suka bayyana farin cikinsu da jin dadin halartar wannan biki da yanayin ruhi.

Shirin "Maulidi Al-Nabi" wanda Mu'assasa "Masoya Annabi (SAW)" ke gudanarwa duk shekara ya zama wata al'ada mai tushe da ake gudanarwa duk shekara a larduna da dama na kasar Turkiyya tare da taken daban.

Shirin na bana mai taken "Shugaban Juriya: Annabi Muhammad (S.A.W) ya samu tarba daga jama'a da dama. An gudanar da bikin ne a dajin Nowruz dake tsakiyar Diyarbakir.

A cikin wannan shirin, masu jawabai sun bayyana muhimmancin inganta wadannan lokuta na addini domin karfafa ruhin addinin Musulunci da hadin kan kasa wajen tinkarar kalubale da rashin adalci da musulmi ke fuskanta a duniya.

 

 

4277808

 

 

captcha