IQNA

Donal Trump Ya Ce Zai Dagewa Kasar Siriya Dukkan Takunkuman Tattalinn Arzikin Da Ta Dora Mata

12:15 - May 14, 2025
Lambar Labari: 3493252
IQNA –Shugaban kasar Amurka Donal Trump ya bayyana cewa zai dagewa kasar Siriya dukkan takunkuman tattalin arzikin da ta dora mata, kuma zai gana da shugaban

Shugaban kasar Amurka Donal Trump ya bayyana cewa zai dagewa kasar Siriya dukkan takunkuman tattalin arzikin da ta dora mata, kuma zai gana da shugaban gwamnatin riko na kasar Ahmad Sharaa wanda aka fi sani da Julani.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto shugaban yana fadar haka a wata tattaunawa da jami’an gwamnatin kasar Saudiya a birnin Riyad na kasar Saudiya, inda ya fara ziyarar aiki a can tun jiya Talata.

Shugaban ya kara da cewa: A yanzu lokaci yayi da mutanen kasar Siriya zasu huta, don zamu dauke dukkan takunkuman da muka dorawa kasar Siriya. Saboda zata samar da huldar Jakadanci da HKI kuma babu wata cuta da zata sami kasar daga Siriya.

Wannan yana zuwa ne bayan da shugaban HKS kuma shugaban gwamnatin riko na kasar ta Siriya bayan kifar da gwamnatin Bashar Al-Asad ya fito fili ya bayyana cewa gwamnatinsa zata samar da huldar Jakadanci da HKI.

Abu Muhammad Al-jula ne, ya kuma gabatar da wani shiri na gina Hasumiyyar Trump a birnin Damascus babban birnin Kasar Siriya don yabawa shugaban.

 

hausatv

Abubuwan Da Ya Shafa: donald trump siriya
captcha