A cikin wata sanarwa da ta fitar ta shafin Al-Zaidi yana cewa: Tattaunawar da dakarun Abbas suka yi ya samo asali ne daga aikin da rundunar aiyuka ta Karbala ta sanya a gaba, bayan gudanar da tarurruka da dama a gaban ministan harkokin cikin gida da babban hafsan soji.
Tun bayan kafuwarta shekaru 11 da suka gabata, rundunar Abbas ta ci gaba da gudanar da tarukan Ashura da Arba'in na Imam Husaini (AS) cikin nasara ta hanyar dakarunta da 'yan sa kai.
Har ila yau, rundunar Abbas Brigade tana taimakawa wajen tsara mashigar kan iyakoki da wuraren ibada wajen bayar da hidima ga alhazai.