A cewar cibiyar yada labarai ta Falasdinu, baje kolin wanda aka gudanar karkashin taken "Ku kalli Idon yaran Gaza" ya kunshi manyan hotuna 10 na kananan yara Palastinawa da yakin Gaza ya rutsa da su, wadanda aka baje kolin a kofar shiga majalisar dokokin kasar.
Tare da wadannan hotuna, alamu masu dauke da sakonni kamar su "Yara ne kawai" da "Shin za mu iya duba idanun yaran Gaza?" aka shigar.
Wasu 'yan kasar Jamus kuma sun nuna juyayinsu ga 'ya'yan Gaza da suka yi shahada ta hanyar ajiye kayan wasan yara kusa da wadannan hotuna.