Manufar wannan taro dai ita ce samar da wani fili da malamai za su yi nazari a kan bangarori daban-daban na yadda Shi'a ke bibiyar kur'ani mai tsarki da kuma duba irin gudumawar da malaman Shi'a suka bayar a fannin karatun kur'ani.
A ranakun 25 da 26 ga watan Satumba ne za a gudanar da taron "Alkur'ani da Shi'a: Rubutu, Nazari, Gado" kamar yadda jadawalin ya zo.