
Idan Muka ɗanɗana wa mutãne wata rahama, sai su yi farin ciki da ita. To, idan wata masĩfa ta sãme su sabõda abin da suka kasance sunã aikatãwa, sai su yi baƙin ciki.
Shin, kuma ba su gani ba cẽwa lalle ne Allah Yanã azurta wanda Ya so daga yalwa, ko Ya tauye arziƙi? Lalle ne a cikin wancan akwai ãyõyi ga mũminai. (Suratul Rum, aya ta 36-37).