Tehran (IQNA) 'Yan gudun hijira Musulman Rohingya da ke sansanoni a yankin Cox's Bazar na kudancin Bangladesh sun yi maraba da matakin da Birtaniyya ta dauka na tsoma baki a shari'ar "kisan kare dangi" da ake yi wa Myanmar a kotun duniya.
Lambar Labari: 3487754 Ranar Watsawa : 2022/08/27
Jagora Ya Yi Kakkausar Kan Halin Da Musulmi Suke Ciki A Myanmar:
Bangaren siyasa, Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei yayi kakkausar suka dangane da shiru da kuma halin ko in kula da cibiyoyin kasa da kasa da masu ikirarin kare hakkokin bil'adama suke yi dangane da kisan kiyashin da ake yi wa musulmin kasar Myammar inda ya ce hanyar magance wannan matsalar ita ce kasashen musulmi su dau matakan da suka dace a aikace da kuma yin matsin lamba ta siyasa da tattalin arziki ga gwamnatin kasar Myammar.
Lambar Labari: 3481889 Ranar Watsawa : 2017/09/13
Bangaren kasa da kasa, wata tawagar masu kai dauki daga kasar Aljeriya na shirin kama hanya zuwa kasar Myanmar domin kai kayan taimakon ga musulmin kasar.
Lambar Labari: 3481280 Ranar Watsawa : 2017/03/03
Bangaren kasa da kasa, Ahmad Tayyib babban malamin cibiyar Azahar da ke Masar ya yi da a kawo karshen zaluncin da ake yi kan musulmi a kasar Myanmar.
Lambar Labari: 3481049 Ranar Watsawa : 2016/12/19