IQNA

Gasar Olampiyad karo na biyu a kasar Rasha da ta kumshi mahangar addinin musulunci

Bangaren kasa da kasa: gasar olampiyad karo na biyu kan mahangar musulunci da harshen larabci za a gudanar a ranekun 18 da 19 na watan Farvardin shekara ta 88 hijira shamsiya a birnin Kazan babban birnin jamhuriyar mai cin gashin kanta ta Tataristan.
Bayan nakaltowa daga majiyar Ria ,cibiyar koyar da Alkur’ani a Iran Iqna ta watsa labarin cewa: wannan gasar ta Olampiyad za ta maida hankali ga jami’oin musulunci a Rasha da cibiyoyi na al’adu,ilmantarwa da koyarwa ta musulunci a wannan kasa kuma a wannan jami’ar musulunci ta Kazan.Burin kaddamar da wannan Olampiyad na musulunci shi sanin yan jami’a da ke a shirye su fahimci addini da koyarwarsa gami da yada shi.
Bayan yan jami’a musulmi a cibiyoyin ilimi na Tataristan akwai yan jami’a daga yankin Ceceniya,Jamhuriyar Kabardino,Balkariya,Maridovuya,NicniNugrad,Masko da sauran yankunan yankin.

359445