IQNA

Masana a Iran za su kubutar da kansu daga mamayar yan danniya na duniya

Bangaren siyasa: Shugaban Jamhuriyar musulunci ta Iran a taron ilimi na fadin Iran ya bayyana cewa: Masana a Iran dole cikin gaggawa a gajeren lokaci su kubutar da kansu daga danniyar masu girman kai na duniya.
A wani rahoto da bangaren siyasa na cibiyar koyar da Alkur’ani a Iran Iqna ya watsa Mahmud Ahmadi Najad a safiyar Laraba 16 ga watan Bahman a taron Ilimi day a hada masana a fadin Iran ya bukace su da su samar da wata sabuwar hanya ga bil adama don yada ilimi da cewa: da taimakon Allah da jagorancin gami da jinjinawar da jagoran juyin juya halin musulunci a Iran a yau Iran ta samu ci gaba da binkasa ilimi da samin jinjinawa ta musamman.

Shugaban na Iran dangane da muhimmancin ilimi da fasaha ta zamani da ake bukata y ace: a kokarin neman ilimi dole ilimi ya kasance karkashin koyarwa ta musulunci da kiyaye dokokin Allah domin ba za mu iya ba mu ringumi ci gaban ilimi da mantawa da koyarwa ta Allah da ka’idodinsa kamar sauran da suka ringumi duniya ya kuma cea a yau da taimakon Allah,da dogaro da hikimomin limaman tsarki da wilaya Iran na samun ci gaba ta fuskar ilimi da kuma hakan zai ci gaba.
359621