Bangaren siyasa: Babbar sakatariyar Jami’ar Zainab (S) a taron bukin tunawa da nasarar juyin musulunci ya bayyana cewa: a yau bayan shekaru talatin da juyin musulunci haskensa ya mamaye duniya kuma tasirinsa ya taimaka ga nasarorin da musulmai ke samu a duniya.
Cibiyar koyar da Alkur’ani a Irna ta Iqna bayan ta nakalto daga bangaren hulda da jama’a a jami’ar Zainab (S) ta watsa rahoton cewa: babbar sakatariyar shirya bukin tunawa da nasarar juyin juya halin musulunci Maryam Behruz ta cewa:Raneku goma masu albarka da a cikinsu aka samar da nasarar juyin juya halin musulunci a Iran karakashin jagoranci Imam Khomeini ® ya taimakawa matana wajen bas u damar taka rawa kuma ya zamewa sauran al’ummomi abin koyi wajen yin adalci da aikata gaskiya dama sauran al’ummomi na duniya.
Ta kara da cewa wadannan raneku na tunatar da ranekun da al’ummar iran suka tashi da bayyana niyarsu ta rungumar koyarwar musulunci karkashin koyarwar Ashura da Imam Khomeini ya jagoranta da hakan ya kawo karshen mulkin danniya kuma Mata sun taka rawa wajen yakar zalumci da gwamnatin danniya.
359584