IQNA

Fim Kan Harin Ta'addancin HARAMTACCIYAR KASAR ISRA'ILA Kan Gaza

Bangaren Kasa da Kasa: Kampanonin Faransa da na Palasdinu suna nan suna shirya fim kan hare-haren ta'addancin Haramtacciyar Kasar Isra'ila a cikin kwanaki 22 kan Gaza da yadda ta yi wa fararen hula kisan gilla da kiyashi.
Cibiyar koyar da Alkur'ani a Iran Iqna bayan ta nakalto daga majiyar labarai ta gidan talbijin Almanar ta watsa rohoton cewa: Atif Isa mai kula da tsara wannan fim kuma shugaban kamfanin gidajen shirya fina-finai ya bayyana cewa: nan ba da jimawa ba za a fara daukan wannan fim din da ya hada da hotunan guraren ban tausayi a Gaza da hakan ke nuni da ta'addancin Haramtacciyar kasar Isra'ila a fili karara. Ya kara da cewa: Wannan Fim ta hadin gwiwa ce tsakanin gidajen fina-finai na Faransa da Palasdinu da ke tabbatar da ta'addancin yahudawan Sahyoniya a fili a kan fararen hula a Gaza a cikin kwanaki 22 da kai hare-hare dare da rana kuma za a yi wannan fim din ne da harsuna hudu( Faransanci,Turancin Ingila,Larabci da Turkanci.

360583