Bangaren Zamantakewa: Hakkokin Iyali a musulunci abin bincike ne a da sanin yadda ya yi daidai da dokokin Iyali a kasashen musulmi.
Cibiyar koyar da Alkur'ani Iqna ce ta watsa rahoton cewa tuni aka shiga shirye-shirye dangane da binciken dokokin hakkin iyali a kasashen musulmi da hakan ke tabbatar da kiyaye hakkin dan adam a kasashen musulmi fiye da sauran kasashen da ba na musulmi a duniya.An kaddamar da makaloli akalla guda bakwai dake bayani kan hakkokin iyali a musulunci kuma wadanda suka gabatar da wadannan makaloli sun fito daga ciki da wajen Iran.
360487